A yayinda kallo ya koma wajen kotun tsarin mulkin kasa, domin jin yadda za ta kaya a game da sakamakon zagaye na 2 na zaben shugaban kasar Nijar na ranar 21 ga watan Fabrairu, wasu kungiyoyin fararen hula a karkashin inuwar OPELE, na kiran kotun da ta yi gaskiya.
An shawarci alkalan kotun su natsu, domin tabbatar da adalci a hukunci, da zasu yanke game da wannan fafatawa da ke ci gaba da haddasa ce-ce-ku-ce a tsakanin magoya bayan Bazoum Mohamed da na Mahaman Ousman.
Shugaban cibiyar tattara bayanan OPELE Maikoul Zodi, yana mai cewa "jami’an da suka aika runfunan zabe domin zuba ido, sun gano wasu tarin kura kurai wadanda a bayyane ka iya shafar sahihancin alkaluman da aka bayar a hukunce, saboda haka suka yi kiran kotun tsarin mulkin kasa ta cire dukkan wani son rai wajen fayyace abubuwan da ta fahimta game da wannan zabe" a cewar Mahamadou Tchiroma Aisami, daya daga cikin jiga-jigan kungiyar OPELE.
Wadanan kungiyoyin sun shawarci hukumar zabe ta CENI ta dauki matakin hukunta mutanen da aka kama da yunkurin bata ayyukan gudanar da babban zaben da ya gabata, ta yadda abun zai zama darasi a nan gaba.
Gungun mambobin OPELE, sun kuduri aniyar shirya wani babban taro domin nazarin hanyoyin da za su bada damar magance matsalolin da aka yi fama da su a yayin zabubukan da suka gabata.
Dalilin da yasa suka bukaci hadin kan masu ruwa da tsaki a sha’anin tsara zabe, wajen tattauna wannan batu na neman karfafa demokaradiyya.
Ana iya sauraron rahoton Souley Moumouni Barma, a cikin sauti.