Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kotu Ta Bayyana Machina A Matsayin Dan Takarar Sanatan Jihar Yobe Ta Arewa


Bashir Machina/Ahmed Lawan
Bashir Machina/Ahmed Lawan

An yi zaben fidda gwanin jam’iyyar APC na mazabar Yobe ta Arewa da aka shafe kusan watanni hudu ana tafka gardama bayan da wata babbar kotun tarayya da ke zama a Damaturu hedikwatar jihar Yobe ta bayyana Bashir Machina a matsayin wanda ya cancanta a cewar jaridar Channels.

Alkalin kotun, Mai shari’a Fadimatu Murtala, ta bayyana hukuncin a yau Laraba.

An shafe watanni ana takun saka tsakanin Machina da shugaban majalisar dattawa Ahmad Lawan mai wakiltar Yobe ta arewa a majalisar dattawa kan tikitin takarar da shi Machina ya samu a zaben fidda gwani da aka gudanar a ranar 9 ga watan Yunin 2022.

Lawan dai ya tsaya takarar shugaban kasa na jam’iyya mai mulki ne a daidai lokacin da zaben fidda gwani na sanata da Machina ya lashe. Shugaban majalisar dattawa, ya sha kaye a hannun tsohon gwamnan jihar Legas, Bola Tinubu, lamarin da ya tilasta masa yin tikitin takarar Sanata amma Machina ya dage cewa ba zai sauka ba.

Sai dai kuma ya yi kokarin karbo tikitin Sanatan Yobe ta Arewa da Machina ya samu, wanda shi kuma Machina ya dage ba zai bar tikitin ga shugaban majalisar dattawan ba.

Lawan ya kasance dan majalisar tarayya tsawon shekaru 23.

Shugaban jam’iyyar APC na kasa, Sanata Abdullahi Adamu, ya yi gargadin cewa Machina na iya fuskantar takunkumi mai tsanani idan har ya ki barin tikitin tsayawa takarar ma Lawan.

Adamu ya yi ikirarin cewa hurumin na jam’iyyar ta koli ne kuma jam'iyyar tana da ‘yancin tantance wanda zai samu tikitin takara a kowane zabe.

A cikin jerin sunayen karshe na ‘yan takarar shugaban kasa da na majalisar tarayya da INEC ta buga a makon jiya Talata, babu sunan wani dan takara da aka buga a Yobe ta Arewa.

XS
SM
MD
LG