Lokacin da gwamna ibrahim Shettime ke karbar kayan tallafi a madadin 'yan gudun hijira dake warwatse a wasu sassan jihar yace nan ba da dadewa ba matsalolin da suka addabi jihar zasu zama tarihi.
Kungiyar masu noman shinkafa tare da wasu suka kawo tallafin domin a rabawa 'yan gudun hijira. Kayan sun hada da kayan abinci da man girki da kayan bukatun yau da kullum.
Gwamnan yace rikicin ya shafi kowane mutum dake cikin jihar kuma zasu yi kokarin ganin cewa matsalar ta kawo karshe. Yace yanzu hakan sun sayi buhun shinkafa fiye da dari shida amma sun kasa rabawa manoma sabili da kalubalen tsaron da manoman ke fuskanta. Idan Allah ya yadda za'a raba masu a daminar badi domin bunkasa harkokin nomansu. Banda shinkafa gwamnatin ta kawo injinan gyara shikafa guda dari shida. Rashin zaman lafiya ya hana rabasu.
Gwamnan ya yiwa mutanen godiya saboda kauna da suka nunawa mutanen Borno.
Su 'yan kungiyar da suka kawo tallafi su ma tashin hankalin ya shafesu to ko menene yasa suka bada tallafi. Alhaji Audu Umar daya daga ikin shugaban kungiyoyin yace sun lura da yawan mutanen da tashin hankalin ya shafa yasa suka ce ba zasu barwa gwamnati kadai ba. Su ma yakamata su taimaka, su ji tausayin wadanda ke gudun hijira.
Ga rahoton Haruna Dauda Biu.