Dubban ‘yan kasar Najeriya da ke gudun hijira a kasashen ketare na kira ga gwamnati da ta kawo masu dauki, ko kuma a yi kokarin maido su gida.
Yanzu haka dai dubban ‘yan Najeriya da sukayi gudun tsira da rayukansu daga wasu garuruwa a arewacin Najeriya Sakamakon rikicin ‘yan boko haram, sun bazu a kasashen ketare da dama, musamman kasashen karamu, da Nijer da Chadi.
Kusan fiye da watanni biyu ke nan da dubban ‘yan Najeriya ke gudun hijira a kasashen na ketare, wasu kuma sun sami damar kubuta suka kwararo zuwa wasu manyan birane ciki harda babban birnin Maiduguri.
Mafi yawancin ‘yan gudun hijirar da suka fada cikin halin kaka-na-kayi suna zaune ne a kasashen na ketare inda babu uwa ba uba, Kuma basu da wani abin yi sai dai dogaro ga Allah. Hakan ya sa ‘yan gudun hijirar ke kokawa ga gwamnatocin jihohi da na tarayyar da su kawo masu dauki.
A hirarrakin da wakilin muryar Amurka Haruna Dauda Biyu yayi da wasu ‘yan gudun hijirar ta wayar tarho, sun fada mashi irin mawuyacin halin da suke ciki na rashin abinci, ruwan sha, da sauran wasu muhimman kayayyaki, kuma wasu lokuta su kan fuskanci wasu ‘yan tashe-tashen hankula a inda suke.
Da aka tuntubi shugaban hukumar samar da agajin gaggwa a arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Ahmed Ganaa ko yana da masaniya akan halin da ‘yan gudun hijirar suka shiga a kasashen waje, kuma wane mataki suka dauka don tallafa masu, shugaban ya tabbatar da cewa ya ji korafin kuma ya kai shi gaba harma sun fara tattaunawa akan yadda za a taimaka ma ‘yan gudun hijirar dake cikin mawuyacin hali sakamakon fadan ‘yan boko haram da kuma yadda za a dawo dasu.