Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojoji Sun Kashe Wasu Matasa a Dururmi, Abuja, Najeriya


Sojojin Najeriya
Sojojin Najeriya

Jiya da daddare sojoji sun kai samame a wata unguwa da ake kira Durumi ta daya cikin birnin Abuja inda suka kashe wasu matasa

Wani da abun ya rutsa dashi yace da daddare sojoji suka fara harba bindiga.

Sanadiyar harbe harben suka fita waje da gudu. A cikin dugun nasu ne sojoji suka kashe wasu cikinsu. Shi ma bai tsira ba domin harsashi ya sameshi.

Ana zargin wani soja mai anini uku da aikatashi daga bataliyan sojojin tsaro ta bakwai dake Abuja. Rahotanni sun bayyana cewa samamen ya hallaka mutane uku kana an raunata wasu da dama. Hakazalika an cafke wasu an kaisu wani wuri da ba'a sani ba.

Wani ganao da baya son a anbaci sunansa yace yana cikin gida yaji an buga kofar gidansa da bindiga an kuma buga tagar gidansa. An ce ya budi sai yaki budewa. Kafin ya farga sai yaran da suke gudu suka tsallaka katanga zuwa cikin gidansa. Sojoji ma suka yi haka nan.

Bayan da sojoji suka shiga gidansa sai suka kama yaran da duka. Da ya ga basu daina ba sai ya fito sojojin suka tambayeshi daga ina ya fito yace daga Jos. Sai suka tambayeshi wane wuri sai yace Mangu. Sai suka ce ya koma dakinsa bashi suke nema ba. Amma ya duba ya ga an tafi da yaran Jos din kusan su takwas. Yace akalla mutanen da aka diba a anguwar sun kai dari da wani abu.

Wani shaida na biyu yace sojojin sun saba kai samame a Durumin ta daya. Wannan samamen ba shi ne na farko ba.

Ga rahoton Medina Dauda.

please wait

No media source currently available

0:00 0:06:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG