Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yunkurin Sanya Sarakuna Cikin Sha'anin Mulki A Najeriya - Hon. Abbas Tajuddeen


Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar
Kungiyar gwamnonin Arewacin Najeriya ta kaddamar da kwamitin hada sarakuna a cikin tsarin mulkin kasar

Duk da kai-komon da aka sha yi don baiwa sarakuna gurbi a kundin tsarin mulkin Najeriya ba tare da nasara ba, sabon shugaban majalissar wakilai a Najeriya, Hon. Abbas Tajuddeen ya ce za su dawo da kudin saka sarakuna cikin sha'anin mulki a kundin tsarin Mulkin Najeriya.

Wannan ne karon farko tun bayan zaben wakilin mazabar Zariya, Hon. Abbas Tajuddeen a matsayin shugaban majalissar wakilai da ya debo tawagar 'yan-majalissun tarayya da na jihohi don zuwa fadar mai-martaba Sarkin Zazzau Ambasada Ahmad a wata ziyara.

Tajuddeen wanda shi ma ya na da mukami na Iyan Zazzau a masarautar, ya ce za su yi duk mai yiwuwa don ganin sarakuna sun sami gurbi a kundin tsarin Mulkin Najeriya.

Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli
Sarkin Zazzau na 19 Ambassador Ahmad Nuhu Bamalli

Dama dai mai martaba Sarkin Zazzau, Ambasada Ahmad Nuhu Bamalli ya nunawa sabon shugaban majalissar wakilan damuwar sarakuna ne kan yadda aka dinga dankwafe kokarin ganin an sama musu gurbi a kundin tsarin Mulkin Najeriya.

Ahmed Nuhu Bamalli
Ahmed Nuhu Bamalli

Mataimakin shugaban marasa Rijaye Hon. Aliyu Sani Madaki na cikin tawagar shugaban majalissar wakilan a fadar Sarkin Zazzau, kuma ya ce za su ba da gudummawar tabbatar da wannan kuduri.

Shi ma shugaban majalisar dokokin Jahar Kaduna, Hon. Yusuf Liman na goyon bayan baiwa sarakuna dama.

Yunkurin saka sarakuna cikin sha'anin mulki a kundin tsarin Mulkin Najeriya dai ya dade yana yawo a majalisu kuma bai taba tsallake dukkan matakai ba ballanta ya kai ga shugaban Kasa.

To shin ko wannan karon kudurin dokar zai kai labari, tun da 'yan majalisar da kan su ke son kai shi? Lokaci kadai ka iya amsa wannan tambaya.

Saurari rahoton a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:53 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG