Kwamishinan ayyukan kiwon lafiya na Jigawa, Dr. Abubakar Tafida, ya ce ya zamo tilas su kara azamar aikin a saboda an samu bullar sabbin kamuwa da cutar ta shan inna wasu jihohi makwabtan Jigawa.
Sai dai har yanzu ba a samu alkaluma na adadin wadanda aka samu nasarar ba su maganin a lokacin wannan aiki ba.
A yunkurinta na kara azamar kawar da wannan kwayar cuta ta Polio, gwamnatin jihar ta Jigawa ta girka karin masu bayar da maganin a tasoshin mota 86 cikin jihar domin tabbatar da cewa dukkan yara masu shigowa cikin jihar ko biyowa ta cikinta, sun samu wannan magani.
A lokacin wannan aikin na Satumba, an sanya malamai da sarakuna da kuma shugabannin kungiyar direbobi ta Najeriya cikin masu zaburar da mutane da kuma taimakawa wajen cimma nasarar aikin.