Wannan tallafi yana zuwa a daidai lokacin da Najeriya take bayyana cewar tana bukatar kimanin Naira miliyan dubu 40, ko Dalar Amurka miliyan 250, domin aiwatar da shirinta na yakar Polio daga shekarar 2013 zuwa 2015.
Babban jami'in diflomasiyya mai kula da ofishin jakadancin kasar Jamus a Najeriya, Klemens Moemkes, shi ne ya bayarda sanarwar wannan tallafin kudin ga Najeriya, jim kadan kafin bukin rattaba hannu a kan yarjejeniyar gudanarwa da kuma samar da kudi kashi na 5 a tsakanin Najeriya da Jamus a Abuja.
A wurin wannan bukin da aka gudanar, har da babban darektan hukumar kula da lafiya tun daga matakin farko ta kasa a Najeriya, Dr. Ado Mohammed, da kuma manaja mai kula da wannan shiri na bankin KFW Bank na kasar Jamus, Dr. Weth Wolfgang. Minista mai kula da ma'aikatar harkokin wajen Najeriya, Frafesa Viola Onwuliri, ita ce ta shirya wannan bukin rattaba hannu kan yarjejeniyar.
Moemkes ya lura cewa wannan tallafin kudin, wani bangaren kokarin da kasarsa ta Jamus take yi ne na tallafawa shirin Najeriya na kawar da cutar Polio.
Yace wadanda za a fi mayarda hankali wajen kaiwa gare su karkashinw annan shirin su ne yara 'yan kasa da shekara 5.