A yayin da ake shirin gudanar da zaben gwamnan jihar Anambra gobe Assabar, kwamitin zaman lafiya na Najeriya da tsohon shugaban kasa Janar Abdulsalami Abubakar ke jagoranta ya shirya wani taron zaman lafiya irin wanda ya saba shiryawa a duk lokacin da za’a gudanar da zabe.
Kamar ko wane taro kuma, an rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya da tabbatar da gudanar zaben cikin lumana, kazalika da kuma aniyar karbar kaddarar sakamakon zaben.
Yarjejeniyar dai na aiki ne a kan jam’iyyun da ke da ‘yan takara a zaben, kuma ana sa ran za ta karfafa wa wadanda suka rattaba hannu gwiwar daukar kwararan matakai na tabbatar da yanayi mai kyau don gudanar da sahihin zabe.
Shugaban hukumar zabe mai zaman Kanta ta Kasa wato INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, na daga cikin mahalarta taron na zaman lafiya wanda kwamitin ya shirya.
Cikin ‘yan takarar da suka sanya hannu a yarjejeniyar akwai Ifeanyi Uba na jam'iyyar YPP, Andy Uba na APC, da Chukwuma Soludo na jam'iyyar APGA.
Sauran sun hada da Valentine Ozigbo jam’iyyar PDP, Godwin Maduka jam’iyyar Accord, Etiaba Chukwuogo na jam’iyyar AA, Nwankwo Chidozie na jam’iyyar AAC, Onyejegbu Okwudili jam’iyyar APM, Ohajimkpo Emeka na NNPP, Ezenwafor Victor na jam’iyya NRM), Nnamdi Nwawuo na PRP, Uzo Godwin na jam’iyyar SDP sai kuma Okonkwo na ZLP.
Tun kafin fara gangamin yakin neman zabe aka yi ta samun hare-haren yan bindiga da ake zargin mambobin haramtaciyyar kungiyar IPOB ne mai rajin kafa kasar Biyafara.
Sakamakon yanayin kalubalen tsaro da ake ciki a yankin kudu maso gabas ya sa babban sufetan ‘yan sanda, Usman Alkali Baba, ya bayar da umarnin hana zirga-zirgar ababen hawa a jihar ta Anambra "don gudanar da zaben dikin kyawawan yanayi."
Hakan na nufin cewa babu motsin ababen hawa ciki da wajen jihar Anambra daga karfe 11:59 na daren Juma'a 5 ga watan Nuwamba zuwa 11:59 na dare a ranar Asabar 6 ga watan Nuwamba da za’a gudanar da zaben kamar yadda gidan talabijan na Channels ya ruwaito.
Gamayyar gwamnonin jihohin kudu maso gabas biyar sun bukaci mazauna yankin da su yi watsi da barazanar rashin tsaro, suna cewa al’umma su fita da kwarin gwiwa a ranar Asabar su jefawa dan takarar da suke so kuri’a.
'Yan takarar dai sun yi gangamin yakin neman zabe ga masu jefa kuri'a na karshe a ranar alhamis kafin zaben na gobe Asabar.
Jihar Anambara, kamar sauran yankin kudu maso gabas, ta sha fama da hare-haren ‘yan bindiga da dama, lamarin da ya sanya shakku kan yadda za’a gudanar zaben na ranar Asabar.
Kungiyar masu fafutukar kafa kasar Biafra wato IPOB ta sha yin barazana kan gudanar da zabuka idan ba'a sako shugabanta, Nnamdi Kanu da ke tsare a hannun hukumar DSS.
Gwamnatin tarayya dai ta ce ta kara karfafa tsaro a jihar Anambra, inda ta yi alkawarin gudanar da sahihin zabe cikin gaskiya da adalci.
Ko a ranar talata, shugaban marasa rinjaye na majalisar dattawa, Enyinnaya Abaribe ya bukaci masu kada kuri’a da su fito a rumfunan zabe, yana mai cewa za’a yi zaben cikin zaman lafiya.