Shugaban hukumar da ke daukan dawainiyar masu yi wa kasa hidima ta NYSC Birgediya Janar Shu’aibu Ibrahim, ya ce mambobin na NYSC suna matsayin jami’an tsaron kasa ne, a dalilin haka za a iya tura su fagen yaki idan bukatar hakan ta taso.
Birgediya Janar Ibrahim, ya bayyana hakan ne yayin wata hira da gidan talabajin na Channels ya yi da shi a shirin hantsi na “Sunrise Daily” a ranar Alhamis.
Kalaman Ibrahim na zuwa ne yayin da ake ci gaba da muhawara kan a soke shirin na yi wa kasa hidima, wanda ya zama wajibi ga duk wanda ya kammala karatun jami’a ko na babbar kwalejin kimiyya ta polytechnic, muddin bai kai shekara 30 ba.
“Mambobin NYSC na mataki ne na zama cikin shirin ko-ta-kwana. Kazalika suna daga cikin tsarin tsaron kasar.” Birgediya Ibrahim ya ce, a wani mataki na nuna adawa da kokarin soke shirin.
“Saboda haka, idan aka tsinci kai cikin yanayi na mummunan yaki, mambobin NYSC suna da ilimi, za a iya horar da su…. tamkar kamar sojoji suke.”
Karin bayani akan: NYSC, Channels, Shugaba Muhammadu Buhari, Nigeria, da Najeriya.
A kwanakin da suka gabata ne majalisar wakilan Najeriya, ta fara muhawara kan kudurin dokar yiwuwar soke shirin, wanda gwamnatin mulkin soji ta Janar Yakubu Gowon ta kirkira a shekarar 1973, a wani mataki na hada kan kasar bayan yakin basasa da Najeriyar ta fuskanta.
Akan tura mambobin na NYSC zuwa sassan kasar har tsawon shekara guda, kafin daga bisani a sallame su, su shiga neman aiki.
Tuni har kudurin dokar neman soke shirin ya kai matakin karatu na biyu a majalisar ta wakilai, amma wasu dama a Najeriyar sun nuna rashin dacewar soke shirin.
Masu goyon bayan a soke tsarin na NYSC a majalisar dokokin kasar, sun gabatar da hujjar cewa, ana jefa rayuwakan masu yi wa kasar hidima cikin hadari, inda da yawa daga cikinsu kan rasa rayukansu.