Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta


Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta.
Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta.

“Ko kudaden da ake biya a da ma da kyar wasu dalibai ke iya biya, mafi akasari sai sun yi aikin karfi kafin su sami biyan kudin makaranta, da yawa daga cikin mu kuma marayu ne.”

Dubban daliban jami’ar jihar Kaduna sun gudanar da wata zanga-zangar lumana, inda suka yi maci zuwa fadar gwamnatin jihar, akan karin da aka yi wa kudin makaranta da dalibai ke biya.

Daliban sun rirrike kwallaye da alluna da ke dauke da sakwanni daban-daban, da suka hada da “a cire karin kudin makaranta,” “mu marayu ne,” "ilmi hakki ne na kowa ba ‘ya’yan masu kudi kadai ba” da dai sauransu.

Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta
Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

Duk da yake dai jami’an tsaro sun hana masu zanga-zangar damar shiga gidan gwamnatin, to amma sun toshe baki dayan titin da ke zuwa fadar gwamnatin jihar, suna rera wakokin gwagwarmaya, da suka hada da na “wajibi ne a samar da ilmi kyauta.”

Wasu musulmai daga cikin daliban masu zanga-zangar ma sun gudanar da sallolinsu a kan titin da suka toshe na zuwa fadar gwamnatin.

Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta
Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

To sai dai daga bisani an baiwa dalibai 3 da ke cikin zanga-zangar damar shiga gidan gwamnati, domin ganawa da jami’ai akan lamarin, inda kuma suka mika takardar kokensu akan karin kudin makaranta, domin isarwa ga gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Daya daga cikin daliban da ya zanta da manema labarai a lokacin zanga-zangar, Comrade Yusuf Shehu, ya yi kira ga gwamnan jihar ta Kaduna da ya sake duba kan matsayinsa na karin kudaden makaranta, ta yadda ‘ya’yan talakawa za su iya samun ilmi.

Ya ce “muna rokon da a soke wannan karin kudin da aka yi, saboda karin na yanzu zai tilastawa dalibai da dama barin makaranta muddin ba’a yi wani abu a kai ba.”

Shehu ya bayyana cewa “Ko kudaden da ake biya a da ma da kyar wasu dalibai ke iya biya, mafi akasari sai sun yi aikin karfi kafin su sami biyan kudin makaranta, da yawa daga cikin mu kuma marayu ne.”

“Roko ne muke yi ba tilastawa ba, domin ko yanayin rayuwa ma na kara ta’azzara, kuma ga shi an kori wasu daga cikin iyaye daga ayukansu, wannan ya kara jefa mu cikin mawuyacin hali,” in ji Comrade Shehu.

Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta
Daliban Jami'ar Kaduna Sun Yi Zanga-Zanga Kan Karin Kudin Makaranta

To sai dai duk da kasancewar zanga-zangar ta lumana ce baki dayan ta, an kafa shingayen jami’an tsaro a kan titin, lamarin da ya takaita zirga-zirga zuwa fadar gwamnatin jihar na dan lokaci.

To sai dai masu fashin baki na tababar tasirin zanga-zangar ga gwamnatin jihar ta Kaduna, a yayin da gwamnan jihar Nasir El-Rufai ya yi sunan dagewa kan matsayar da duk ya dauka, wacce yake ganin ita ce daidai a jihar.

Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai
Gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai

A makon da ya gabata ma daliban sun gudanar da irin wannan zanga-zangar, amma a harabar jami’ar kawai da ke kan titin Tafawa Balewa.

Haka kuma makwanni biyu da suka gabata, kungiyar kwadagon Najeriya ta gudanar da wata gagarumar zanga-zanga da ta dakatar dukkan al’amura a jihar ta Kaduna, domin kalubalantar matakin gwamnatin jihar na korar daruruwan ma’aikata a jihar.

Duk da ya ke dai gwamnatin tarayya ta sa baki, har ma da kiran bangarorin biyu a teburin sasantawa, har kawo yanzu ba’a kai karshe ba akan matsalar ta gwamnatin jihar da kungiyar kwadago, ko da yake dai an sami dage yajin aikin bayan kwanaki 3 ana yin sa.

Kawo yanzu kuma gwamnatin jihar ba ta yi martani ba akan korafin daliban.

XS
SM
MD
LG