A yau Talata, ma’aikatan ceto a Indonesia, sun ci gaba da ayyukan neman gawarwakin fasinjoji da ma’aikatan jirgin Lion Air da ake tsammanin sun mutu, bayan da jirgin ya abka cikin teku.
jirgin ya fadi ne mintina kadan da tashin shi daga filin jirage na Jakarta da safiyar jiya Litinin.
A daren jiya, jami’ai sun ce an kai sassan jikin mutane asibiti cikin wasu jakunkunan gawa 24, domin a tantance su.
Sannan an gano daruruwan kayayyaki mallakar fasinjojin a sashin da jirgin ya fadi, wadanda suka hada da litattafai, karamar jakar adana kudi, jakankuna, wayoyin salula da sauransu.
Daga cikin fasinjojin da suka mutu, har da yaro karami da kuma wasu jirarai biyu.
Akalla gwanayen ninkaya 40 aka tura karkashin ruwa domin neman ragowar jirgin na Lion Air, wanda ya bace daga na’urar da ke bibiyar jirage, mintina 13 da tashin shi.
Shugaban da ke jagorantar binciken, Muhammad Syaugi ya ce “Muna amfani da wata na’ura mai hasken gaske, domin neman duk wani abu da ke karkashin ruwa, muna kuma fatan za mu gano inda ainihin gangar jikin jirgin take.”
Ana dai tunanin wannan bangaren jirgin, na can zurfin mita 30 zuwa 35 a karkashin ruwa a cikin Tekun na Java.
Hukumomi, sun ce gabanin hadarin, matukin jirgin ya nemi da ya koma filin tashin jiragen da ya taso.
Wannan hadari shi ne na farko da ya taba rutsawa da irin wannan jirgi kirar Boeing 737 MAX 8, wanda aka inganta shi ake kuma tururuwar sayen shi.
Facebook Forum