Albarkacin wannan rana da Majalisar Dinkin Duniya ta kebe, an bukaci kasase su tashi tsaye domin kawar da wariya don ganin an tabbatar da adalci a tsakanin al’umma, a daidai wannan lokaci da ake fama da annobar coronavirus.
Hukumar wanzar da zaman lafiya ta Nijar da ake kira Haute Autorite a la Consolidation de la Paix ta shirya wani gangami a birnin yamai, domin wayar da kan al’umma kan muhimmancin zaman lafiya.
Taken wannan rana ta bana shine a tashi tsaye domin kawar da wariya don tabbatar da adalci mai dorewa a ko ina a duniya.
A cewar Abdoulaye Balde jami’i a sashen kula da sha’anin tsaro da zaman lafiya a reshen hukumar MMD mai kula da ci gaban karkara wato UNDP, taken ya yi dai dai da halin da ake ciki a yau a duniya, saboda haka gudunmawar kowa na da matukar mahimmanci wajen samar da zaman lafiya mai dorewa da kwanciyar hankali wani aiki ne da ya shafi kowa da kowa.
Yanayin da ake ciki a yau a wasu kasashen duniya musamman a yankin Sahel wani abu ne dake kara tabbatar da tasirin adalci a tsakanin jama’a.
Domin nuna misali mai kyau, hukumar wanzar da zaman lafiya ta shirya wa nakasassu gudun tseren kekuna da ya gudana lokaci guda kuma a wuri daya da gudun tseren da ta shirya domin majiya karfi albarakcin wannan rana.
A yanzu haka kasashe kimanin 100 ne ke jiran tallafin alluar riga kafin cutar coronavirus daga manyan kasashe duniya, a wani lokacin da aka dade dada rarrabawa wasun miliyoyin alluran riga kafin wannan anoba lamarin da MDD tace ya na bukatar gyara kamar yadda a wani bangare ya zama wajibi a taimakawa wadanda wannan masifa ta haifarwa koma baya a harkokinsu na yau da kullum da wadanda aika aikar ‘yan bindiga ta durkusar da komai nasu a yankuna da dama.
Domin karin bayani saurari rahotan Sule Muminu Barma: