Ranar laraba da ta wuce kotun kolin Amurka ta saurari muhawara daga bangaren masu goyon baya da masu adawa kan dokar da gwamnatin Jihar Arizona ta kafa kan bakin haure, wacce ta janyo cece kuce. Koda ta ina hukuncin kotun kolin ya kaya kan wan nan batu, hakan zaiyi matukar tasiri a bangaren doka da kuma siyasa.
A harabar kotun kolin masu zanga zanga daga duka bangarorin biyu, masu goyon baya da masu adawa da dokar gameda bakin haure sun bayyana yadda suke ji gameda dokar ba ta rera wakoki ba kadai amma har da addu’o’i.
“Muna rokon ka Allah ka mana jagora da wadanda suke cikin wan nan gini suke muhawara a yau din nan.”.
Alkalan kotun kolin sun saurari muhawara daga bangarorin biyu kan wan nan doka da aka kafa da nufin magance korarowar bakin haure, wadanda jihar Arizona take kiyasin yawansu ya kai dubu dari hudu da suka shiga jihar ba bisa ka’ida ba.
Daya daga cikin sharuddan dokar itace baiwa ‘yansanda damar su binciki ko mutum yana da izinin kasancewa cikin kasar, bayan sun tsaida shi kuma suka zaci cewa yana cikin kasan nan ba bisa ka’ida ba. Wani bangaren dokar ya shar’anta cewa laifi ne idan bakon haure ya yayi cikin jihar ko ya nemi aiki.
A cikin masu goyon baya dokar ta Arizona a harabar kotun kolin har da Ken Moreau, dan sanda a jihar Maryland.
“Tilas mu takaita bakin haure.Ba kawai kasarmu tana da hakki ba, ya ma wajaba akanta ta takaita bakin haure,domin ganin muna da mutane milyan 11-12 bakin haure wadanda suke cikin kasar nan ba bisa ka’ida ba, wan nan babbar matsala ce”.
Haka kuma masu goyon bayan dokar sun ce an tilastawa jihar ta dauki matakin kare kan iyakokinta domin gwamnatin tarayya ta kasa yin haka.
Haka ma George Pope wanda yake da zama a jihar Virginia makwabciyar gundumar Columbia shima yayi zanga zangar nuna goyon baya ga dokar a harabar kotun kolin.
(( POPE ACT: “At this particular time it is……))
“A wan nan marra batun ya fi kasancewa ja in ja kan hakkin da jiha take da shi da kuma hakkin gwamnatin tarayya, gwamnatin da bata fuskanci matsaloli da muke fuskanta akan iyakokinmu ba, saboda haka aka shiga yanayi na rudani gameda bakin haure”.
Gwamnatin shugaba Obama ta kai karar jihar Arizona, ta kuma hana wasu sassan dokar aiki bayan da kotunan kasa suka amince da matsayar gwanatin tarayyar, tana mai cewa hakkin kare kan iyakoki hurumin gwamnatin tarayya ce ba ga daidaikun jihohi ba.
Sai dai a lokacin da lauyoyin suke muhawara, alkalan kotun da dama sun nuna alamar kamar zasu goyi bayan jihar Arizona cewa ‘Yan sanda suna da damar su tambayi duk wanda suka tsayar takardun izinin kasancewa cikin jihar .
Haka suma masu adawa da dokar sun fito da karfinsu a harabar kotun kolin, cikinsu harda Rev. mari Castellanos, wata shugaba a hadaddiyar cocin almasihu, wacce suka kaura zuwa Amurka daga Cuba tun tana ‘yar yarinya.
((CASTELLANOS ACT: “When I came to this country……))
“ Lokacinda nazo kasan nan, an karbe ni hanu biyu biyu kuma aka buda mini hanyoyi masu yawa saboda gwamnatin Amurka bata kaunar gwamnatin Cuba. Kasan me ya faru, sai kawai harkoki na suka mike gadan gadan. Dukkanmu mukayi karatu har zuwa jami’a. Dukkanmu harkokinmu sun bunkasa, kuma abinda zai faru kenan idan aka karbi bakin haure.
Ha kazalika masu adawa da dokar suka ce gayawa ‘Yan sanda su nemi takardun izinin kasancewa cikin kasa idan suka tsaida mutum, zai bada damar a tsaida mutum ba domin ya aikata laifi illa saboda jinsinsa. Ga abinda Luis Gutierrez na jam’iyyar Democrat dan majalisar wakilai ta tarayya mai wakilatar jihar Illinois.
((GUTIERREZ ACT: “The fact is we have outlawed racial…..))
“Gaskiyar magana an haramta tsaida mutum bisa la’akari da jinsinsa. Yin haka ya sabawa doka. Tambayar anan itace shin kotun kolin Amurka zata karfafa hakkinda ‘yan kasa suke da shi na yin tattaki ba tareda an tsangwamesu ko an dakatarda su aka musu tambayoyi saboda launinsu ko irin lafazinsu ba?
Yadda za a tunkari matsalar bakin haure ya zama batun siyasa a zaben shugaban kasa da za a yi bana, kuma lamari ne da ya dami hispaniwa ‘yan kasa a duk fadin Amurka, rukunin mutane da yawansu yake ta karuwa a Amurka.
Wasu jihohi ma sun kafa dokoki shigen na Arizona, kuma suna dokin ganin hukuncinda kotun koli zata yanke, ana sa ran kotun zata sanarda hukuncinda ta yanke cikin watan Yuni.