Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yau Take Ranar Yara Mata Ta Duniya


PLATEAU: Ranar 'yan yara mata ta duniya.
PLATEAU: Ranar 'yan yara mata ta duniya.

Majalisar Dinkin Duniya (MDD) ta ware duk ranar 11 ga watan Oktoba domin domin nazari kan ci gaba da kuma kalubalen da suke fuskanta a fadin duniya, taken wannan shekarar shine Muryata Makomarmu Daidai.”

Wannan muhimmiyar rana ce ta yin nazarin bukatu da kuma matsaloli da yara mata ke fuskanta, tare da neman hanyoyin da za a tabbatar musu da hakkinsu.

Duk kuwa da ci gaban da aka samu a fadin duniya cikin shekaru sama da ashirin da suka gabata, domin tabbatar da cewa duk wata yarinya na rayuwa cikin koshin lafiya da walwala, akwai aiki mai yawa a gaba.

A jihar Kaduna ta Najeriya, an samar da wata doka mai tsanani wajen hukunta duk wanda aka kama da laifin yiwa yara mata fyade.

Haka kuma dubban yara mata a Arewa maso Gabashin Najeriya, ke fama da kalubalen rashin matsugunni a sanadiyar rashin tsaro da ayyukan ‘yan bindiga suka haifar.

Mata Da Yara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Fufore
Mata Da Yara A Sansanin 'Yan Gudun Hijira Na Fufore

Bisa ga wani binciken Hukumar Lafiya Ta Duniya (WHO), ana yiwa miliyoyin yara mata aure kafin su cika shekaru 18 a duniya. Haka kuma, a fadin duniya yarinya ‘daya cikin biyar na fuskantar cin zarafi na lalata.

A Gabashi da Kudancin nahiyar Afirka, kusan kashi 80 cikin 100 na sabbin kamuwa da kwayar cuta mai karya garkuwar jiki ta HIV yara mata ne.

FILE - Yara Mata a Makarantar Sakandare
FILE - Yara Mata a Makarantar Sakandare

Taken wannan rana ta wannan shekarar 2020, shine “Muryata, Makormarmu Daidai.” Wannan kira ne mai jan hankali ganin an tattauna kalubalen da suke fuskanta, musamman ma bangaren lafiyarsu da kuma ‘yancin su har ma da gudunmawar da za su ke bayarwa wajen samar da sauyi a duniya.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG