Hukumar Lafiya Ta Majalisar Dinkin Duniya ta ware a matsayin ranar fadakar da al’ummar duniya game da illar da cutar Malaria ke yiwa bil Adama a sassa daban-daban na duniya, musamman ma kasashe masu tasowa.
Najeriya da daya daga cikin jerin kasashen da ke fama da cutar, lamarin da ke haifar da mutuwar mata da kananan yara msuamman ma a yankunan karkara.
Taken bikin na bana shine “A shirye muke domin kawar da cutar Malaria” a wani rahoto da hukumar lafiya ta MDD ta fitar ya nuna cewa mutune kusan rabin miliyan ne suka rasa rayukansu a shekara ta 2016 sakamakon kamuwa da cutar Malaria. Yayin da mutum miliyan 216 suka kamu da cutar.
Hukumar lafiya ta duniya ta ce ana kashe kusan dalar Amurka Biliyan uku wajen samar da magunguna da sauran magani na rigakafi. Kasashe da yawa na duniya na daukar matakan da suka dace bayan na MDD domin kawar da cutar ko kuma neman saukinta ga bil Adama.
A Najeriya dai an dauki matakai da dama da suka hada da rage farashin maganin cutar zazzabin cizon sauro, tare da samar da gidajen maganin sauro mai dauke da magunguna domin rigakafin cutar, wanda ake bayar da su a asibitoci da daban-daban na kasar.
Domin karin bayani saurari cikakken rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum