A bayan ganawar gaggawa da aka yi a tsakanin shugaba Muhammadu Buhari da manyan jami'an tsaron kasar, an yanke shawarar kaddamar da wani sabon atusayen soja da aka sanya ma suna "Operation Cat Race" a wasu jihohi na arewa ta tsakiyar Najeriya.
Kakakin fadar shugaban ta Najeriya, Femi Adesina, ya fada cikin wata sanarwa cewa a cikin wannan makon za a kaddamar da wannan atusayen wanda aka tsara da nufin kawo karshen fitinar da ake fama da ita a tsakanin makiyaya da manoma a jihohin.
Wakilin Muryar Amurka, Umar Faruk Musa, yace manyan hafsoshin dukkan bangarorin sojan Najeriya, da na 'yan sanda da jami'an tsaron farin kaya sun bayyana bukatar dake akwai ta daukar matakan shawo kan wannan lamari tare da sace-sacen mutane da ake yi a wadannan jihohin.
Wani tsohon hafsan soja, Janar Abdulrazak Umar, yace a yawancin lokuta a irin wannan lamarin, a kan samu matsaloli a fannoni biyu ne, ko dai ba a fayyace takamammen abinda ake son cimmawa ba, ko kuma wannan aiki bai fada hannun wanda zai iya gudanar da shi yadda ya kamata ba.
Tsohon hafsan na soja ya fadawa Umar Faruk Musa cewa a wasu lokutan, dalilai na siyasa suke hana daukar matakan da suka dace na shawo kan irin wannan fitina da Najeriya take fama da ita.
A yanzu dai, 'yan najeriya sun sanya idanu domin ganin irin tasirin da wannan atusaye zai yi wajen shawo kan rikicin tsaro a yankin arewa ta tsakiyar.
Facebook Forum