Babban kwamandan rundunar yaki da Boko Haram ta Operation lafiya Dole, Manjo janar Rogers Nicholas, wanda ya bayyanagodiya sosai ga irin tallafin da kungiyoyin agaji masu zaman kansu ke bayarwa ga 'yan gudun hijira a arewa maso gabashin Najeriya, ya kuma bayyana damuwa game da ayyukan da wasunsu ke yi.
A lokacin da yake magana a wajen taron hukumomin tsaro da na kungiyoyin agaji da ya kira a hedkwatar rundunar dake Maiduguri, Janar Nicholas yace akwai wasu kungiyoyi marasa rajista da suka shiga cikin yankin wadanda kuma ayyukansu ke gurgunta sha'anin tsaro baki daya.
Ya gargadi irin wadannan kungiyoyi da su yi rajista cikin sati biyu ko kuma ba za a sake kyale su su shiga cikin sansanonin 'yan gudun hijira ko kuma su wuce ta hanyoyin da sojoji ke gadinsu ba.
Kwamandan ya roki dukkan kungiyoyin agaji dake aiki da su tabbatar da cewa su na yin amfani da motoci masu lafiya wajen jigilar kayan agaji domin gujewa yadda motoci ke lalacewa cikin daji har 'yan Boko Haram su samu sukunin bullowa su sace kayan dake ciki.
Haka kuma ya bukace su da su guji yin katsalanda a harkokin da ba na su ba.
Facebook Forum