Musulmi kimanin miliyan biyu da rabi sun hallara a Mina, su na hawan Dutsen Arafat, domin gudanar da aikin Ibada mafi tsarki na Hajjin bana a kasar Sa'udiyya.
Mahajjatan zasu wuni yau litinin a kan Dutsen Arafat, wanda ke gabas da birnin Makkatul Mukarrama, domin ibada da addu'o'i. A wannan wuri ne Annabi Muhammad (Sallalahu Alaihi Wasallam) ya gabatar da hudubarsa ta karshe, shekaru fiye da dubu da dari hudu da suka shige.
Daga nan Arafat, alhazai zasu doshi Muzdalifah, kafin su komo Mina gobe talata domin aikin jifar Shedan, aikin ibadar da ake gudanarwa da nufin kawar da ayyukan shedan daga zuciyar alhaji ko hajiya.
Alhazai su na takawa da kafa ko a cikin motocin safa, ko na tasi. A bana, an kaddamar da kashin farko na wani jirgin kasa da aka kirkiro musamman domin rage cunkoso a kan titunan mota na kasar ta Sa'udiyya.
Wannan layin dogo na jirgin kasa da wani kamfanin kasar China ya gina kan wata farfajiya, ya fara aiki yau litinin, inda yake daukar alhazai tsakanin Mina ya bi ta Muzdalifah zuwa Dutse Arafat. A bana, wannan jirgin kasa zai rika daukar sulusin fasinjojin da zai iya dauka ne idan an kammala aikin gina shi baki daya.
Aikin Hajji na daya daga cikin shika-shikan addinin Musulunci, wanda aka bukaci dukkan Musulmin dake da hali, da iko, da karfin zuwa da ya je shi akalla sau daya a cikin rayuwarsa.
Za a iya sauraron rahoton Murtala Faruk Sanyinna kan yadda mahajjatan Najeriya suke gudanar da hawan Arafat yau litinin a saman wannan labarin daga hannun dama.