Musulmi fiye da miliyan biyu ne suke ci gaba da saukowa daga kan Dutsen Arfa a kasar Sa'udiyya, inda za su fuskanci ayyukan ibada na gaba a aikin Hajjin bana da suke yi.
Litinin da sanyin safiya mahajjata sanye da harami na fararen sutura suka fara hawa Dutsen a gabas da birnin Makka domin salloli da addu'o'i. A nan Dutsen Arfa ne Annabi Muhammad (saw) ya gabatar da hudubarsa ta karshe shekaru fiye da dubu daya da dari hudu da suka shige.
A cikin hudubar da yayi da azahar din litinin, babban shaihin malami na kasar Sa'udiyya, Abdulaziz al-Sheikh, ya roki Musulmi da su guji tashin hankali, da yaki, da bambancin akida, sannan su rika tausayawa 'yan'uwansu.
A cikin daren nan, alhazai zasu kwana a Muzdalifah inda zasu tsini duwatsu kafin su koma Mina da safiyar talatar nan inda za su gabatar da aikin jifar shedan.
Shugaba Barack Obama na Amurka, da maidakinsa Michelle Obama sun aike da gaisuwa da sakon fatar alheri ga Musulmi na duniya baki daya, a madadin illahirin al'ummar Amurka. har ila yau shugaban na Amurka da maidakinsa sun yi ma dukkan alhazai na bana fatar zasu yi aikin Hajji lafiya su kuma koma kasashe da gidajensu lafiya.