Ministan harkokin cikin gida na Faransa, Brice Hortefeux, yace kasar Sa’udiyya ta yi gargadin cewa kasashen Turai, musamman ma kasar Faransa, su na fuskantar wata barazanar ta’addanci daga kungiyar al-Qa’ida. Hortefeux ya fadawa gidajen rediyo da telebijin na Faransa a jiya lahadi cewa a cikin ‘yan kwanakin nan hukumomin leken asiri na kasashen Turai suka samu wannan gargadin daga hukumomin Sa’udiyya.
Yace wannan barazana ta zahiri ce, kuma gwamnati ta daura damara.
A farkon wannan wata Amurka da Britaniya da kuma Japan suka gargadi ‘yan kasashensu game da yiwuwar fuskantar hare-haren ta’addanci a Turai a bayan da jami’an leken asiri na kasashen yammaci suka bankado wata makarkashiyar da tsagera masu alaka da kungiyar al-Qa’ida a Pakistan suke kullawa ta kai hare-hare a manyan biranen kasashen Britaniya da Faransa da kuma Jamus.
Jami’an suka ce hare-haren su na iya yin kama da na 2008 da aka kai a Mumbai a kasar Indiya, inda aka kashe mutane 166 aka raunata wasu da da