'Yan siyasar Najeriya suna yaba yarjejeniyar zaman lafiya a lokcin zabe da kuma bayan zabe da shugaba Goodluck Jonathan da kuma Janar Muhammadu Buhari, da sauran manyan 'yan siyasa suka sanya hanu akai a Abuja, domin tabbatar an kaucewa duk wani abunda zai haifar da rashin zaman lafiya da sunan rikcin zabe.
Tsohon Gwamna kuma senata Danjuma Goje ya yaba da yarjejeniyar, yace lokaci yayi da Najeriya zata shiga sahun kasashen da suka ci gaba kamar Ingila da Amurka, inda ake gudanar da zabe cikin lumana.
A nata banagaren Rundunar 'Yansandan Najeriya tace a shirye take ta dauki duk mataki da ya wajaba kan 'yan siyasa wadan da suke son wargaza Najeriya domin kawai suna neman zaba shugaban kasa ko Gwamna.
Ga karin bayani.