Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Ya Kai Ziyara Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno


Shugaba Goodluck Jonathan.
Shugaba Goodluck Jonathan.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya kai ziyara Maiduguri, babban birnin jihar Borno inda rikicin Boko Haram ya daidaita don gane ma kansa halin da ake ciki.

Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya je Maiduguri, babban birnin jihar Borno a wata ziyara ta gane wa kai dangane da halin da ake ciki a jihar game da batun tsaro, musamman ma sanadiyyar hare-haren kungiyar Boko Haram mai tsattsauran ra’ayin addini.

Wakilinmu a Maiduguri Haruna Dauda ya bi tawagar Shugaban kasar kuma ya bayyana ma abokin aikinmu Ibrahim Alfa Ahmed abubuwan da ke gudana. Haruna ya ce ga dukkan alamu cikin wuraren da Shugaban kasar zai ziyarta har da barikin soji, inda zai gana da sojoji sannan ya kuma ziyarci sansanonin ‘yan gudun hijira biyu, musamman ma inda aka tsugunar da wadanda aka kwaso daga garin Baga. Haruna ya tabbatar ma Ibrahim cewa bay akin nemar zabe Jonathan ya je yi a Maiduguri ba, ya ce ziyarar ta Shugaban kasar ba ta rasa nasaba da irin sukar da mutane ke ta yi na rashin cewa uffan da Shugaban kasar ya yi tun bayan harin da kungiyar Boko Haram ta kai garin Baga duk kuwa da yada batun da ake ta yi a fagagen labarai da majalisin jama’a.

Dangane da batun tsaro kuwa, Haruna ya ce akwai ma jiragen sama da ke shawagin kare tawagar Shugaban kasar. Ya ce banda haka ma, Shugaban kasar ya iso da dogarawan tsaro na musamman don kare Shugaban kasa.

Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan Ya Kai Ziyara Maiduguri, Babban Birnin Jihar Borno - 2'16"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:16 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG