Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Matakan Gudanar da Zabe Cikin Lumana


'Yan sandan Nijeriya a bakin aiki.
'Yan sandan Nijeriya a bakin aiki.

An cigaba da tarurrukan jaddada muhimmancin gudanar da zabukan 2015 cikin kwanciyar hankali.

A jiya ne gidauniyar Kofi Anan ta tsohon Sakatare Janar na Majlisar Dinkin Duniya ta shirya taro da ‘yan takarar shugabancin najeriya a karkashin jam’iyyu daban daban, inda har-ma a karshen taron suka rattaba hannu akan yarjejeniyar tabbatar da cewa an gudanar da zabukan dake tafe a kasar cikin kwanciyar hankali da lumana.

A hannu guda kuma,ran Litinin din da ta gabata Mataimakin Sifeto janar na ‘Yan sandan Najeriya Mai Kula da Shiyya ta Daya, wadda ta kunshi Jihohin Kano da Katsina da kuma Jigawa, Alhaji Tambari Yabo Mohammeed yayi taro da shugabannin jam’iyyu a jihohin uku, kana kuma a jiya Laraba ya yi wata ganawa da gwamnan jihar Jigawa Sule Lamido duka dangane da yadda za a yi zaben ba tare da tarzoma ba.

Daga bisani wakilinmu a Kano, Mahmud Ibrahim Kwari ya tattauna da mataimakin shugaban ‘yan sandan akan abubuwan da suka cimma, in da ya ce, “Sanin kowa ne cewa zabe na kara kusatowa, don haka mun kira su ne don mu kara yin masu gargadi kan tanajin da dokar zabe ta yin a cewa ana so a yi zabe cikin kwanciyar hankali babu aikata laifukan da dokar zabe ta hana, misali yaran da ba su wuce shekaru 18 ba su shiga zabe; ko kuma a yi zabe a ba da sakamako sannan a je a tare jami’an INEC da jami’an tsaron da ke masu rakiya zuwa inda za a sake tattara shi don a fadi sakamako na karshe.”

Alhaji Tambari Yabo ya ce a wannan taron da aka yi, an dada jaddada ma mahalarta taron cewa aikata duk wani laifin da dokar zabe ta hana bai dace ba ko muskala zaratun. Alhaji Yabo ya ce akasarin mahalarta taron na nuna alamar fatan cewa abubuwan da su ka faru a shekara ta 2011, musamman ma abubuwa masu nasaba da tashe-tashen hankula, ba su sake faruwa ba. Da aka tambaye shi musabbabin ganawarsu da Gwamnan Jihar Jigawa Sule Lamido, babban jami’in ‘yan sandan ya ce duk dai abubuwa ne masu nasaba da tsaro.

Matakan Gudanar da Zabe Cikin Lumana - 2'00"
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:00 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG