An gayyaci yaran makarantar da su gabatar da zane-zane da za a iya yin amfani da su wajen karfafa sakon kyamfen yaki da Polio, inda zane-zanen kowane yaro zai taimakawa asusun UNICEF wajen samun kudin sayen maganin rigakafin cutar Polio da niyyar kare wani yaron dagfa kamuwa da ita.
Wani kamfanin hada-hadar ayaba a kasar Ireland mai suna Fyffes, shi ne yake daukar nauyin wannan gangami, inda ake fata makaranatu da dama a Carlow zasu shiga sahu.
A tsakiyar watan nan na Maris za a aike da cikakken bayanin wannan gasar zane-zane ga makarnatun yankin, kuma dukkan zane-zanen da suka yi nasara, to za a buga su domin amfani wajen yayata wannan shiri na yaki da Polio a duk fadin kasar Ireland.