Masanan suka ce a wancan lokacin ma, mutane sun yi ta nuna turjiya a lokacin da ake kokarin kawar da cutar agana baki dayanta, amma daga baya da suka gane amfanin rigakafin, jama'a sun rungume shi hannu bibbiyu, aka kuma samu nasara.
A cikin 'yan kwanakin nan, jami'an lafiya na duniya sun zaga Najeriya baki daya kaf, amma ba a samu rahoton mai fama da cutar kurkunu ba ko guda daya, abinda ya sa a yanzu aka ayyana Najeriya a zaman wadda ta kawar da cutar. Wannan ma an samu nasarar hakan ne ta hanyar rigakafi.