Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Yara Nakasassu Miliyan Uku Ba Sa Zuwa Makaranta a Najeriya


Wasu yara marayu suna karbar tallafi
Wasu yara marayu suna karbar tallafi

Asusun tallafawa kananan yara na Majalisar dinkin Duniya UNICEF, ya ce daga cikin yara miliyan 10 da bas a zuwa makaranta, fiye da miliyan uku daga cikinsu yara ne masu fama da nakasa.

Hakan kuma na faruwa ne saboda rashin ababan da za su saukaka musu gudanar da rayuwarsu cikin sauki a makarantun, a cewar gamayyar kungiyoyin nakasassu da ake kira JONAWD a takaice.

A kasashe masu tasowa musamman a nahiyar Afrika ba kasafai ake maida hankali kan bukatun masu nakasa ba, watakila kom saboda halin ko in kula da hukumomi ke nunawa ko kuma ana karkata kudaden da aka ware domin hakan.

Ire-ire wadannan kalubale kuma na haifar da cikas ga yadda musamman yara nakasassu ke gudanar da rayuwarsu a fannonin daban daban kamar a makarantu.

Dalilin haka Jummai Ali ta tattauna da mai baiwa shugaban kasa shawara kan harkokin nakasassu a Najeriya, Dr Samuel Ankeli, inda ta fara da tambayar shi, dalilan da ya sa adadin yaran nakasassu da ba sa zuwa makarnata ya kai har miliyan uku:

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:35 0:00
Shiga Kai Tsaye

XS
SM
MD
LG