Haka kuma wasu na ganin cewa da sun canza salo wajen zama ‘yan kungiyar jin ‘kai ga ‘yan gudun hijira, wasu ma da yawa na nuna damuwa kan dagewa akan kwato ‘yan matan makarantar Chibok kadai, ba tare da ana ambatar sunayen sauran mata da yawa da aka sace a Arewa maso Gabashin Najeriya ba.
Yarinya ta biyu da aka kwato a Danbua Serah Lukas bayan Amina Ali-Nkeki, hakan ya kawo ya kawo tababa daga ‘yan gwagwarmayar, dake cewa bata daga cikin ‘yan mata da ake nema kafin ayi bayanin ‘yan makarantar Chibok ce daga Madagali a jihar Adamawa.
Daya daga dattawan Arewa maso gabashin Najeriya, Alhaji Musa Yola, na nuna damuwa ga yadda ‘yan gwagwarmayar kan tafiyar da kamfen dinsu. Inda yace in gaskiya meyasa sojoji ba zasu jagorancesu zuwa dajin Sambisa ba? yace abinyi yanzu shine addu’a kan cewar Allah ya fitar da su.
Wakilin Muryar Amurka Nasiru Adamu El-Hikaya dake Abuja, ya tambayi shugaban kungiyar Chibok na Abuja, Sambido Wazaya kan aikin gwagwarmayar inda ma yace basu gamsu ga yadda duniya ke basu hadin kai wajen kwato sauran ‘yan matan ba, idan an dauke jami’ar difilomasiya Samantha Power da shugaba Obama ya turo kan lamarin.
Saurari cikakken rahotan Nasiru Adamu El-Hikaya.