A jihar Bauchi al’umomin karamar hukumar Itas-Gadau sun kwana cikin alhini da kuma juyayin mutuwar wasu yara 18 ciki har da 'yan mata 16, yayin da wani kwale-kwale ya kife da su.
Bincike ya yi nuni da cewa yaran sun gamu da hatsarin ne akan hanyarsu ta zuwa roron shinkafa, kamar yadda hakimin Itas, Zannan Tafidan Katagum, Alhaji Mustafa Abba ya shaida wa Muryar Amurka ta wayar tarho.
A wata hira da Muryar Amurka, Dan majalisar dokokin jihar Bauchi mai wakiltar mazabar karamar hukumar Itas-Gadau, Bala Labiru Kashuri, wanda ya halarci jana’izar yaran da suka rasa rayukansu a sanadiyar kifiwar kwale-kwalen, ya bayyana lamarin a matsayin iftila'in da basu taba ganin irinsa ba a yankin. Ya kuma ce mutane 28 ne a cikin kwale-kwalen amma 18 daga cikinsu ne suka rasu.
A gefe guda kuwa tawagar gwamnatin jihar Bauchi a karkashin jagorancin mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela, ta kai ziyarar gane wa ido inda hatsarin ya faru.
Ga Abudulwahab Muhammad da cikakken rahoton:
Facebook Forum