‘Yan tawayen Libiya sun fara kai hari kan wata matatar mai a wani garin da ke dab da yammacin birnin Tripoli, a wani yinkuri na fatattakar dakarun da ke biyayya ga Mu’ammar Gaddafi don su cigaba da dannawa zuwa babban birnin kasar.
Matatar man da ke Zawiyya, mai tazarar kilomita 50 daga birnin Tripoli, na daya daga cikin wurare kalilan da dakarun gwamnati da kuma mutanen cikin babban birnin ke samun man fetur. Wani kwamandan ‘yan tawayen y ace babban bututun da ke kai mai daga matatar zuwa birnin Tripoli, an katse shi, to amman ba a tantance wannan ikirarin ba tukunna.
Rahotanni daga garin Zawiyya na nuna cewa ‘yan tawayen na rike da da dama daga sassan birnin. Yau Laraba ma dakarun da ke goyon bayan Gaddafi sun yi barin wuta kan birnin a daidai kuma lokacin da dakarun dakarun Gaddafi da ke lab eke ta harbi kan ‘yan tawayen.
A jiya Talata, ‘yan tawayen sun yi watsi da wani rahoton da ke nuna cewa sun tattauna da wani na hannun daman shugaban na Libiya.
Shugaban Majalisar Wuccin Gadin Shugabancin Kasar, Mustafa Abdel Jalil, y ace babu wata tattaunawa au ta kai tsaye au a fakaice da aka yi da wani wakilin Gaddafi, kuma tattaunawa irin wannan ba ma abu mai yiwuwa ba ne, sai ko in shugaban na Libiya ya sauka.