‘Yan tawayen Libya na barazanar yin kawanya wa Trabulus babban birnin kasar, bayan sun kwace wasu muhimman garuruwa a kudu da kuma yammacin birnin kuma suna kokarin katse muhimman hanyoyi a kokarinsu na tilasta wa Shugaba Muammar Gaddafi sauka daga gadon mulki.
‘Yan tawayen sun ce suna rike da mafi yawan Zawiyya, wanda wani muhimmin gari ne da ked a tazarar kilomita 50 daga yammacin Trabulus, inda karfin Gaddafi yak e. Mayakan ‘yan tawaye sun shiga Zawiyya ran Asabar wanda wannan shi ne lokacin das u ka fi dannawa kusa da babban birnin tun bayan da gwamnati ta murkushe ‘yan tawayen Zawiyya a mako na farko da fara zanga-zangar.
Dakarun da ke goyon bayan Gaddafi sun yi musayar wuta a garin Zawiyya ranar Litini, a wani kokari na korarsu tun daga tsakiyar birnin.
Mai magana da yawun ‘yan tawayen ya kuma ce mayakansu sun kama garuruwan Surman mai tazarar kilomita 60 daga yammacin Trabulus, da kuma Gharyan mai tazarar kilomita 80 daga kuduncin babban birnin. To sai dai ba a iya tantance ikirarin nasu ba.
Iko da Zawiyya, da Surman da Gharyan zai taimaka wa ‘yan tawayen su iya katse Trabulus daga muhimman hanyoyi daga kudu da kuma wani da ke kai wag a Tunisia daga Yamma.