Kungiyar yan ta’addan Taliban sun mamaye birnin Ghazni, wani gari mai tazarar kilomita 150 daga kudu maso yammancin Kabul a daren Alhamis. Mummunan fada ya ci gaba tsakanin kungiyar yan ta’addan da jami’an tsaron gwamnati har zuwa safiyar yau jumu’a.
A wani lokaci, duka bangarorin biyu suna fada ne a tsakiyar garin kusa da wani ginin gwamnati mai muhimmanci, wanda ya hada da ofishin gwamna da cibiyar tsaro ta kasa, da cibiyar bincike ta Afghanistan a cewar mazauna wajen da wani jami'in gwamnati Amanullah Kamrani.
Gwamnati ta tura mayaka na musamman na Afghan wadanda suka taimaka wajen kora 'yan Taliban bayan gari a cewar janar Farid Mashal, babban jami’in 'yan sandan yankin. Duk da haka yace yan ta’addan suna samun mafaka a cikin gari, wanda ke sa aikin 'yan sanda yana zama mai wahala. Mazauna garin sun ce fadan ya ci gaba a wasu bangarorin garin musamman a unguwa ta biyu.
Facebook Forum