Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Kungiyoyin Agaji Sun Yi Tur Da Harin Da Saudiyya Akan Yamal


Yara da suka jikata
Yara da suka jikata

Kungiyoyin agaji na kasa da kasa sun fusata tare da yin Allah wadai da harin da Saudiyya ta jagoranta akan kasar Yamal wanda ya hallaka akalla mutane 43, akasarinsu yara ne a yankin 'yan Houthi dake tawaye

Kungiyoyin da ke gudanar da ayyukan agaji irin su Save the Children, da Doctors Without Borders, suna ci gaba da nuna matukar fushinsu tare da yin Allah wadai da dakarun da Saudiyya ke jagoranta wajen kai hare-hare akan ‘yan tawayen Houthi, wadanda suka halaka akalla mutum 43 a ranar Alhamis a Yemen, wadanda aksarinsu kananan yara ne.

Akalla mutum 60 ne suka jikkata bayan ga wadanda suka mutu.

Daya daga cikin makaman masu linzami da aka harbo, ya fada akan wata motar bas dauke da kanana yara yayin da suke komawa gida daga wani yawon shakatawa da makarantarsu ta shirya.

Hotunan talbijin, sun nuno kananan yara a asibiti jina-jina, wadanda sanadiyar dimuwar da suka shiga har ta sa har ba sa iya kuka, yayin da wasu ke ta birgima a kasa suna jiran a kai musu dauki

Amurka dai na goyon bayan dakarun da Saudiyyan ke jagoranta, wadanda ke kaikaitar ‘yan tawayen Houthin na Yemel da ke samun goyon bayan Iran.

Mai magana da yawun ma’aikatar harkokin wajen Amurka, Heather Nauert, ta ce “sun yi na’am da suka ce za su binciki wannan lamari, kuma suna samun hadin kansu.”

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG