Wannan ba mamaki ya kawo karshen rashin ayyana takarar ta Jonathan da wasu masu son mulki ya dawo arewa da wuri ke bukata, don in Jonathan ya koma zai shekara 4 ne.
Babban lauya mazaunin Lagos Femi Falana ya tsaya kan cewa Jonathan ba shi da hurumin takarar don an rantsar da shi har sau biyu a matsayin shugaban kasa, amma shi kuma babban lauya Mike Ezkekhome ya ce a’a Jonathan na da hurumin, da hakan ya biye wa masu cewa ai rantsuwar Jonathan ta farko ta kammala wa’adin mulkin marigayi Umaru ‘Yar’adua ce.
Goodluck Jonathan wanda a ke ganin sa da shugaba Buhari kuma a zaben gwamnan Bayelsa ma ya mara baya ga David Lyon na APC duk da wani dalili ya ba wa dan PDP Daauye Diri nasara, hakanan an daina ganin sa a dukkan tarukan PDP.
Tsohon darakta a gwamnatin tarayya mai mara baya ga shugaba Buhari, Abdulkarim Muhammad ya yi mamakin saya wa Jonathan fom.
A na sa bangaren shi ma tsohon babban daraktan gidajen rediyon Najeriya Ladan Salihu wanda dan PDP ya ce ashe APC ta gane alherin Jonathan.
A kan samu mutane da kan ce sun fi son lokacin cin hancin da a ke zargi na zamanin Jonathan da jan siterin gwamnatin Buhari da su ka ce ba a sauka a tashar nasara ba.
APC dai za ta gudanar da zaben fidda gwani a karshen watan nan da mafi yawan ‘yan takara a tarihin siyasar Najeriya. Yayin da wannan labari ya karade duniya da jan hankalin masu sharhi, ofishin Jonathan, ta hannun mai taimaka ma sa kan labaru, Ikechukwu Eze ya fitar da sanarwa cewa Jonathan bai san da wannan sayen fom din ba. Hasalima bai ba da umurnin a saya ma sa ba.
Sanarwar ta kara da cewa a matsayin Jonathan na tsohon shugaba har ya na son takara ba zai bi ta gefe ba, zai fito ne ta shararrar hanya.
Yayin da ya nuna hakan tamkar cin fuska, duk da haka ya gode wa masu son ya fito takarar.