A cikin karshen makon jiya ne rahotannin karkashin kasa suka bayyana cewa, gwamnan na Kano ya amince tare da zabar mataimakin sa Nasiru Yusuf Gawuna ya gaje shi a zaben da za’a gudanar badi idan Allah ya kai mu.
Baya ga haka, gwamna Ganduje ya ayyana tsohon kwamishinan kananan hukumomin da lamuran masarautu na Kano, Murtala Sule Garo a matsayin dantakarar mataimakin Nasiru Yusuf Gawuna.
A wani taron magabata da kuma shugabannin Jam’iyyar da marecen ranar Talata, gwamna Ganduje ya ce baya ga biyayyar mutanen biyu da kwarewar su a fagen mulki da siyasa, rawar da suka taka a dambarwar zaben gwamna na shekara ta 2019 a Kano, wadda aka yiwa lakabi da Inconclusive, ta kara armashin cancantar su ta zama gwamna da mataimaki.
Yanzu haka dai an fara samun mabanbantan ra’ayi dangane da wannan mataki a tsakanin ‘yayan Jam’iyyar ta APC a Kano. Aminu Ibrahim dan Jam’iyyar APC ya yi na’am da matakin gwamnan inda yake cewa Gawuna shine mafi cancantar zama dan takarar gwamna a jami’iyar APC saboda kokarinsa da kuma girmama ‘ya’yan jami’iya kana mutum ne wanda bai taba rigima da kowa ba a jami’iyar.
Sai dai ra’ayin Alhaji Isa Abdullahi Dazino, dan Jam’iyyar ta APC a Kano ya saba ma na Ibrahim, yana mai cewa idan aka yi la’akari da girmar APC da mutanen dake neman wannan kujera bai yiwuwa a ce wadannan mutane kadai suka fi cancantar zama kan kujeran. Ya kuma kara da cewa hanyar da aka bi aka zabo su ta sabawa tsarin dimokaradiya.
Wannan dai shine karo na biyu da gwamna mai sauka ya baiwa mataimakin sa takara domin ya gaji shi, a jihar Kano, inda a shekara ta 2015 gwamna Rabiu Musa Kwakwaso ya tsayar da gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Daga Kano ga rahotan Mahmud Ibrahim Kwari: