Dama wadannan ‘yan takarar Boakai da Weah sune ke sahun gaba a zaben da aka gudanar na 10 ga watan oktoba, inda Weah ya samu kashi 38.4 yayin da Boakai ko ya samu kashi 28.8. Ganin babu wanda daga cikinsu ya samu adadin da ake bukata don samun rinjaye, hakan ta sa dole ne a sake zagaye na biyu na zaben.
Sai dai an samu tsaiko, domin kotu ce ta bada umurnin cewa da za a gudanar da zaben ne ranar 7 ga watan Nuwamba. Wacce ke marawa Weah baya a matsayin mataimakiya ita ce Sanata Jewel Howard-Taylor, tsohuwar matar shugaba Charles Taylor da ya haifarwa kasar yaki a cikin shekarar 1989.
Yanzu haka dai Taylor yana zaman gidan yari har na tsawon shekaru 50 a kasar Birtaniya bayar rawar da ya taka a rikicin kasar Saliyo. Sai dai har yanzu Taylor yana da dimbin magoya baya a cikin kasar ta Liberia, kuma ana zargin cewa wannan matar ta tsohon shugaban kasar da take neman zama mataimakiyar Weah idan suka ci zabe, ita ce ta taimaka masa samun nasarar yawancin gundumomi a zaben farkon da aka gabatar.
‘Yan takarar biyu dai suna gina yakin neman zabensu ne bisa batun samar da aikin yi ga ‘yan kasa da inganta ilmi da samar da ababen more rayuwa. Amma kuma a wuri daya wasu masu sukar Boakai dan shekaru 73 da haihuwa na cewa, bai tabuka komai a tsawon lokacin da ya kwashe a matsayinsa na mataimakin shugabar kasa Sirleaf.
Yayin da shi kuma George dan shekaru 51, masu sukarsa ke cewa ba shi da wata kwarewa akan harkoki mulki. Masu kula da harkokin yau da kullum sun ce zai yi wahala a sami sakamakon zaben cikn dan kankanin lokaci.
Facebook Forum