Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Pakistan Uku Sun Mutu A Wata Musayar Wuta Da Na India


'Yan Sanda Na Tambayar Wani Dalilinsa Na Son Wucewa Ta Shingen Tsaro A Daya Daga Inda India Ke Da Iko.
'Yan Sanda Na Tambayar Wani Dalilinsa Na Son Wucewa Ta Shingen Tsaro A Daya Daga Inda India Ke Da Iko.

Sojojin kasar Pakistan guda uku aka kashe a wani hari da sojojin India suka kai a jiya Litinin, a yankin Kashir inda kasashen biyu ke takaddama akansa.

Sojojin Pakistan sun fada yau Talata cewa sun bude wuta ne biyo bayan sabawa wata yarjejeniyar dakatar da bude wuta ne da aka karya, abinda yasa sassan biyu suka budewa juna wuta.

Sai dai India tace sojojin na atisaye ne kwatsam sai suka ji sojojin na Pakistan sun dirar musu. Sakamakon wannan musayar wutar ba a samu sojan kasar India ko guda da ya mutu ba, amma a ranar asabar din data gabata sojojin India guda hudu aka kashe a Pakistan sakamakon tsallake wani layin da suka ce ya raba tsakaninsu.

Haka kuma a ranar Litinin din sojojin Indiyan sun kashe wani Noor Mohammed Tantray, shugaban ‘yan gwagwarmayar sa kai mai suna Jaish-e-Mohammed a garin Srinagar da ke kusa da birnin Kashmir.

Wanda ya mutu sakamakon wani fada da ya barke tsakanin ‘yan kungiyar da ‘yan sanda a wajen birnin wannan gari, kamar yadda ‘yan sandan suka bayyana.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG