Kungiyar ta Afenifere ta bayyana matsayar ta ta ne a wani taronta da take yi wata-wata, ta bakin shugabanta Cif Ayo Adebanjo, inda ta ce shugabannin kungiyar sun yi matsayar cewa muddin ba’a samar da sabon tsarin mulki ba, to kuwa ba za’a gudanar da zaben shekarar 2023 ba a dukkan yankin Yarbawa a Najeriya.
Da yake zantawa da manema labari jim kadan bayan kammala taron na wannan wata a Sanya-Ogbo da ke cikin jihar Ogun, Adebanjo ya ce ya zama bata lokaci ga al’ummar Yarbawa su shiga zabe mai zuwa a karkashin tsarin mulkin shekara ta 1999.
Ya bayyana cewa lokaci yayi da za’a yi bitar kundin tsarin mulki, domin daidaita wasu rikitattun al’amura kafin lokacin babban zaben shekara ta 2023.
Shugaban na Afenifere ya ce al’ummar Yarbawa basu da amanna akan kundin tsarin mulkin da ke aiki a Najeriya a halin yanzu, haka kuma ba za su yi amanna da zaben za’a gudanar a karkashinsa ba.
Dangane da aikin yin garambawul da majalisar dokokin Najeriya ke yi kuwa, Adebanjo ya ce hakan ba zai magance kalubalen da ke kasa ba.
“Za’a gudanar da zabe a karkashin gurbataccen tsarin mulki. An ce majalisar dokoki za ta yi gyaran alhali ita kan ta majalisar gubatacciya ce. Kenan kana bukatar mai cin gajiyar matsala ya yi gyara akan matsala, da wa kake magana kenan?” in ji shugaban na Afenifere.