Ba sabon batu bane samun baraka tsakanin magoya bayan jam'iyun siyasa idan suka gudanar da zabuka har dai in an saba dokoki ko ka'idojin jam'iya.
To sai dai masana kimiyar siyasa na ganin ya kamata a ce dimokradiyar Najeriya ta wuce irin wannan matakin na samun baraka sanadiyar zabe, domin shekaru sama da ashirin da ta yi ta isa tashi daga zama jaririyar dimokradiya.
Zabukan da jam'iyar APC ta gudanar kwanan nan dama na makonnin baya sun bar baya da kura a wasu jihohi domin korafe-korafe suna son ruruta wutar husuma tsakanin ‘ya'yanta kamar abin da ke faruwa a Sokoto inda aka yi zabe biyu na bangarori biyu a jam'iya daya.
Honourable Abdullahi Balarabe Salame dan majalisar wakilai ne kuma yana cikin masu fafatuka a dayan bangaren, ya ce shugabannin ba su gudanar da zabukan akan ka’ida ba, amma su sun gudanar da zaben yadda ya kamata dalilin da ya sa aka gudanar da zabe biyu.
Shi kuwa shugaban riko na jam'iyar na jaha Isa Sadiq Achida yace ba haka lamarin yake, don ba su suka gudanar da zabe ba.
To ko yaya masana ke kallon wannan dambarwa? a ganin Farfesa Tanko Yahaya Baba, ‘yan siyasa ba su damu da harkokin rayuwar jama’a ba.
Masana dai na cike da mamakin ganin yadda har yanzu ‘yan siyasar Najeriya ke yawo da hankulan jama'a maimakon a hada kai a yi wa talaka aiki.
Saurari rahoto cikin sauti daga Muhammadu Nasir: