Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Shi'a Suna Zanga-Zangar Kwanaki Uku A Abuja


ABUJA: Gangamin 'Yan Shiya
ABUJA: Gangamin 'Yan Shiya

A yau ne mabiya tafarkin shi'a daga sassa daban daban na Najeriya suka fara wani gangami na kwanaki uku a birnin Abuja don nuna juyayin rikicinsu da sojoji a Zaria.

Idan dai ba a manta ba, tun bayan rikicin ‘yan shi’ar ne da sojojin Najeriya a Zaria aka cafke shugaban nasu Sheikh Ibrahim Yaqub El-Zakzaky bayan rasa rayukan mabiyan Malamin da dama ciki har da ‘ya’yansa da aka zargi sojojin da kashe su.

A watannin baya wata kotu a Najeriya ta bada umarnin sakin Shehin Malamin tare da gina masa sabon gida a inda yake so sakamakon rushe masa muhallin da aka yi.

Bugu da kari kuma a bashi diyyar Miliyoyin Nairori sakamakon cin zarafin da aka masa. To amma duk da wannan hukuncin na kotun, sakin El-Zakzaky ya ci tura. Wanda hakan ce ta sa mabiyan nasa ke ta zanga-zangar lumana don ganin an sake shi.

Ko a wannan ranar ma, mabiyan na El-Zakzaky sun bayyana cewa za su ci gaba da zanga-zangar lumana har sai an ji kukansu bisa dokar sakin Malamin nasu da aka zartar amma jami’an gwamnati da alhakin sakin nasa ya rataya a kansu suka yi burus da lamari.

Wakilinmu Hassan Maina Kaina ya halarci waje zanga-zangar a cikin rahon nan da ya aiko mana cikin murya.

'Yan Shi'a Sun Shirya Zanga-Zangar Kwanaki Uku A Abuja - 2:30
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:17 0:00

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG