An gurfanar da mutumin da ya tayar da wani bam jiya litinin a tashar jirgen karkashin kasa na birnin New York a gaban kotu, inda aka tuhume shi da laifin yin barazanar ta'addanci.
Rudunar yan sanda ta New York ta fada dazu cewa Amurka an tuhmi Akayed Ullah mai shekaru 27 da haihuwa da laifin mallakar makami ta hanyar da ta saba wa doka.
Hukumomin sun ce Ullah, wanda ya yi kaura zuwa Amurka daga Bangladesh, kuma tshon direban tasi, ya yi amfani da igiyoyin roba da wata laida wajen daura bam din a jikinsa yiya litinin, amma kuma bam din bai tashi gaba daya bha.
Jami'an kiyaye bin doka da oda suka ce ya kalli faya fayen farfanganda na kungiyar Da'esh a kan intanet, ya kuma fadawa masu bincike cewa ya aikata wannan abu ne a saboda cin zalin sojan da Amurka take yi.
Facebook Forum