Hukumar ‘yan sandan ciki a Nijeriya ta ce ta damke sama da mutane 100 da ake zargin ‘yan kungiyar Islama mai dauke da makami da ke arewacin Nijeriya din nan ne, da wasu jiga-jiganta.
Jami’an hukumar basu ambaci sunan kungiyar ba, to amman kungiyar Boko Haram kan dau alhakin kai munanan hare-hare a jihohin arewacin Nijeriya shida, ciki har da kashe-kashen gilla da kuma hare-hare kan ofisoshin ‘yan sanda. Hare-haren sun hada da harin bam da aka kai a watan jiya kan hedikwatan ‘yan sanda Nijeriya da ke Abuja.
Ma’anar Boko haram dai it ace, “Ilimin Yammacin Duniya Haramun Ne.” Kungiyar na son ta wanzar da shari’ar Islama a arewacin Nijeriya.
Shugaban Nijeriya Goodluck Jonathan ya yi tayin tattaunawa da kungiyar, to amman ya zuwa yanzu kungiyar ta ki.
‘Yan sanda a birnin Maiduguri na arewacin Nijeriya na farautar wadanda su ka kai jerin harbe-harbe da hare-haren bam das u ka halla mutane 10 ranar Lahadi.
Babu dai wanda ya dau alhakin kai harin to amman ‘yan sanda na zargin ‘yan Boko Haram.