Majalisar ministocin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ta fara aiki wannan makon inda akasarin tsofaffin ministocin suka koma ma’aikatunsu na da. Shugaba Jonathan yace sauya ministoci a kai-a kai da ake yi ya sa wadansu barin ma’aiaktun tun kafin su koyi yadda zasu gudanar da ayyukansu. Dalili ke nan da ya mayar da akasarin ministocinshi. Tsofaffin ministocin sun hada da ministocin manyan ma’aikatu kamar ma’aikatar tsare-tsare, ma’aikatan kula da albarkatun man fetir da kuma ma’aikatar shari’a. Shugaba Jonathan zai yi sauyi a ma’aikatar kudi inda zai ba manajin darektar babban bankin duniya Ngozi-Okonjo-Iweala, wadda ta taimaka aka yafewa Najeriya wadansu basusukan da ake binta lokacin tana ministar kudi a shekara ta dubu biyu da biyar, ana kuma kyautata zaton za a kara mata karfin ikon gudanar da harkokin kudi. Shugaba Jonathan yana kokarin yiwa kamfanin man fetir na kasar garambawul ya kuma yi alkawarin samar da karin ayyukan yi ta wajen bada karfi kan bunkasa kamfanoni. Babbar kalubalar da gwamnatinshi ke fuskanta ita ce hare haren da mayakan Islama suke kaiwa a jihohin arewacin kasar wadanda suka ce suna yaki domin ganin an kafa shari’ar musulunci a kasar.
Majalisar ministocin shugaba Goodluck Jonathan na Najeriya ta fara aiki wannan makon inda akasarin tsofaffin ministocin suka koma ma’aikatunsu na da.