Hukumar tsaro ta Najeriya ta bada labarin kama mayakan sakai 100 dangane da jerin hare hare a fadin jihohi dake arewacin kasar. Kakakin hukumar SSS Marilyn Ogar tace hukumomi sun kama fiyeda kwamandojin rassa su dari a jihohin Bauci,Borno, Kaduna,Kano, Yobe da kuma Adamawa.
Oga tace saboda matakan tsaro ba zamu bada karin bayani kan wadanda aka kama ba, domin har yanzu ana ci gaba da wayar musun da kai, haka kuma muna kokarin shawo kansu sabo da su koma cikin al’uma.
Kame kamen ya biyo bayan kai wa wasu mashaya a birnin Maiduguri hari cikin makonni biyu da suka wuce har suka kashe akalla mutane 30. Babu wadda ya dauki alhakin kai hare hren, amma ana zaton kungiyar nan ta ‘yan Boko Haram mai matsanancin ra’ayin Islama ce take da alhakin kai hare haren.
Ogar tace ba a gurfanar da ko mutum daya ba cikin wadanda aka kama, domin abinda ta kira matakan “rarrashi” da shugaba Goodluck Jonathan ya ayyana da nufin shawo kan tarzomar.
Kasancewarsu ‘yan Najeriya koda menene damuwarsu, sun wuce gona da iri. Matakin farko shine jawo hankalinsu domin kawar da su daga kan wan hanya, inji Madam Oga.
Har zuwa yanzu dai kungiyar Boko Haram taki amsa tayin shugaba Jonthan na tattaunawa, tana cewa babu yadda za’a yi su tattauna yayinda jami’an tsaron suke neman murkushe su.