Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sanda Na Bincike Kan Kisan Mutum 15 A Rikicin Manoma Da Makiyaya A Jihar Nasarawa


Yan Sandan Najeriya.
Yan Sandan Najeriya.

Rikicin manoma da makiyaya kan albarkatun ruwa da filayen kiwo, na daya daga cikin kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

‘Yan sanda a jihar Nasarawa sun ce ga dukkan alamu kashe-kashen na ramuwar gayya ne, bayan mutuwar wani bafulatani makiyayi da aka kai wa hari da adduna.

Ana yawan samun tashe-tashen hankula tsakanin manoma da makiyaya kan yin amfani da fili.

Kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Nasarawa, Ramhan Nansel, ya ce hukumomi sun aike da jami’an tsaro na hadin gwiwa da suka hada da ‘yan sandan sashen yaki da ta’addanci da sojoji zuwa yankin da lamarin ya faru.

Ya ce abu ne da ba a saba gani ba a samu rikicin kabilanci tsakanin manoma da makiyaya a yankin, kuma hukumomi na jan hankalin makiyaya da manoma wajen tattaunawar zaman lafiya, yayin da ake ci gaba da bincike.

Maharan sun mamaye kauyukan Takalafiya da Kwaja da ke gundumar Karu da yammacin ranar Alhamis, inda suka yi ta’addanci kan mutanen kauyen na tsawon sa’o’i kamar yadda mazauna yankin suka bayyana.

Rikicin manoma da makiyaya kan albarkatun ruwa da filayen kiwo, na daya daga cikin kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya, kasar da ta fi yawan al'umma a nahiyar Afirka.

A cikin shekarar 2018, kungiyar Amnesty International ta ce kusan mutane 4,000 ne aka kashe a fadan da aka shafe tsawon shekaru uku ana yi. Kungiyar ta ce rashin binciken matsalar da gwamnati ke yi na kara ruruwa rikicin.

Hukumomin kasar sun aike da ta'aziyya ga iyalan da lamarin ya shafa, inda suka yi alkawarin hukunta wadanda suka aikata laifin, tare da taimakawa wajen samar da kayayyakin agaji ga mutanen da aka kona gidajensu.

‘Yan sanda sun ce harin ramuwar gayya ne bayan da aka kashe wani makiyayi mai shekaru 18 da harbin bindiga a kai, a wannan yanki kwanaki biyu da suka gabata.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari zai mika mulki a wannan watan, inda sabon shugaban kasa Bola Tinubu zai maye gurbinsa.

Zababben shugaban kasa, Tinubu zai gaji kasar da har yanzu take fama da ayyukan ta’addanci a yankin arewa maso gabas da kungiyoyin masu garkuwa da mutane domin neman kudin fansa da aka fi sani da ‘yan bindiga, a yankin arewa maso yamma da tsakiyar kasar.

XS
SM
MD
LG