Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

TARABA: Wani Bom Ya Jikkatu Mutum 3 a Jalingo


Wasu mata ta wundo suna kallon wata majinyata da harin bom din da aka kai a Jalingo ya shafa a asibiti
Wasu mata ta wundo suna kallon wata majinyata da harin bom din da aka kai a Jalingo ya shafa a asibiti

Rundunan 'yan sandar jihar Taraba ta tabbatar da tashin wani abu mai karar gaske a wata mashaya da ke anguwar Daurawa a karamar hukumar Jalingo, babban birnin jihar Taraba.

Jami’an ‘yan sandan jihar sun ce bom ne kirar hannu, kuma yayi sanadiyar jikkata a kalla wasu mata uku.

Daya daga cikinsu wadda ta fi jin rauni yanzu haka tana jinya a asibitin kwararru da ke Jalingo, yayin da sauran biyun kuma aka sallame su daga asibitin nan take.

Kakakin Rudunar 'yan sandan jihar, S.P. Usman Abdullahi, ya shaida wa Muryar Amurka cewa yanzu haka jama'in tsaro sun killace wurin da lamarin ya auku don hana jama'a mu'amalla da wannan yankin.

Bom da ya fashe a anguwar Daurawa a karamar hukumar Jalingo, babban fadar jihar Taraba
Bom da ya fashe a anguwar Daurawa a karamar hukumar Jalingo, babban fadar jihar Taraba

Wani mai sharhi kan lamarin tsaro a Nijeriya, Kwamred Umar Usman, na ganin ya kamata gwamnatin jihar ta hada kai da jami'an 'yan sanda jihar domin gano inda ake hada wadannan bom na gargajiya.

Ya ce hakan shine zai kawo karshen yawan tashe-tashen wadannan ababen.

Saurari rahoton Lado Salisu Garba a sauti:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:26 0:00

XS
SM
MD
LG