Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

'Yan Sandan Iran Sun Kama Mutane 30 A Wani Samame Kan Taron Bautan Shaidan


Wasu da aka kama a taron.
Wasu da aka kama a taron.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, an kama maza 18 da mata 12 a wani taro a lardin Mazandaran da ke arewacin kasar, ba tare da bayyana lokacin da aka kai harin ba.

Hukumomin Iran sun kama wasu mutane 30 da ake zargi da kasancewa 'yan kungiyar bautan Shaidan ne a wani taron da aka yi ta "shaye-shayen barasa", kamar yadda kafafen yada labarai na kasar suka ruwaito yau Alhamis a wani samame na baya bayan nan.

Kamfanin dillancin labaran Fars ya bayar da rahoton cewa, an kama maza 18 da mata 12 a wani taro a lardin Mazandaran da ke arewacin kasar, ba tare da bayyana lokacin da aka kai harin ba.

Jami'an 'yan sanda sun kwace "barasa da kwayoyi" tare da gano wasu "alamun bautar shaidan" a wurin taron, in ji shugaban 'yan sandan lardin Davood Safarizadeh.

Ya kara da cewa mahalarta taron sun yi bulaguro daga wasu larduna zuwa wurin.

Hare-hare kan taron da ake kira "taron bautan Shaidan" ba bakon abu ba ne a cikin kasar mai ra'ayin mazan jiya, galibi ana kai hari kan shagulgulan shaye-shaye, wanda aka haramta a kasar..

A ranar Asabar, 'yan sanda sun tsare mutane 35 a wani hari makamancin haka a lardin Khuzestan da ke kudu maso yammacin kasar, kuma a cikin watan Mayu, an kama mutane fiye da 250 da suka hada da Turawa uku a yammacin Tehran babban birnin kasar saboda yada "shaidan".

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG