Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Kashe Mayaka Masu Goyon Bayan Iran 12 A Wani Harin Da Isra'ila Ta Kai Kusa Da Aleppo Na Kasar Syria


Akalla mayaka masu goyon bayan gwamnatin kasar Iran 12 ne aka kashe a wani harin da Isra’ila ta kai cikin dare kan wata masana’anta da ke kusa da Aleppo a arewacin Syria, kamar yadda wata kungiya mai zaman kanta ta sanar a safiyar yau Litinin.

Kungiyar kare hakkin bil'adama ta Syria ta ce, an kashe mayaka 12 masu goyon bayan Iran daga Syria da wasu kasashen ketare a wani hari da jiragen yakin Isra'ila suka kai a wani wuri a garin Hayyan da ke arewacin Aleppo, inda suka tayar da bama-bamai a wata masana'anta.

Ma'aikatar tsaron kasar ta Siriya a cikin wata sanarwa da ta fitar ta ce "da tsakar dare ne Isra'ila ta kaddamar da farmaki ta sama daga kudu maso gabashin Aleppo, inda suka nufi wasu wurare" da ke kusa da birnin, inda ta kara da cewa "harin ya janyo shahidai da dama da kuma barnar dukiya".

Syria Aleppo Destruction
Syria Aleppo Destruction

A cewar kungiyar Observatory wacce ke da hedkwata a Biritaniya, amma tana da tarin majiyoyi a cikin Syria, an tura masu aikin ceto da masu kashe gobara zuwa wurin domin kula da wadanda suka jikkata tare da kashe wutar da ta tashi.

Isra'ila ta kai daruruwan hare-hare a kan makwabciyarta ta arewa tun bayan barkewar yakin basasar Siriya, inda aka fi kai hare-hare kan sansanonin sojoji da mayakan da Iran ke marawa baya, ciki har da 'yan kungiyar Hezbullah.

Yakin Syria dai ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da rabin miliyan tare da raba wasu miliyoyi da muhallansu tun bayan barkewarsa a shekara ta 2011 bayan da Siriya ta murkushe masu zanga-zangar kin jinin gwamnati.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG