Da yake yi wa manema labarai bayani kan abin da ya faru, kakakin rundunar ‘yan sandan DSP Kamal Abubakar, ya ce sun sami labarin matasan sun fito suna gudanar da zanga-zanga ba tare da samun izini ba.
Hakan ya sa jami’an ‘yan sanda suka tarwatsa masu zanga-zangar tare da kama mutane biyar.
Yanzu haka dai an saki mutanen da aka kama.
Sai dai hukumomin tsaro na ganin ba laifi bane gudanar da zanga-zanga idan har an cika sharudan da aka tanadar.
A na su bangaren, jagororin matasan sun ce sun fito ne domin nunawa gwamnati rashin jin dadinsu ganin yadda aka kwashe shekaru uku da fara wasu ayyukan gina tituna, ganin irin kudaden da gwamnatin jiha ke samu.
Matasan dai na ikirarin cewa a baya sun taba sanarwa da jami’in ‘yan sanda amma kuma aka hanasu fitowa yin zanga-zangar, wanda hakan ya sa a wannan karo suka fito ba tare da neman izini ba.
Saurarin martanin da gwamnatin jihar ta Bauchi ta mayar, a wannan rahoto na Abdulwahab Muhammad:
Facebook Forum