Kwamishinan ‘yan sanda na jihar Legas Mr. Imohimi Edgal, shi ne ya tabbatar da hakan a lokacin da yake nunawa manema labarai makaman da aka kama. Haka kuma kwamishinan ya bayyana cewa an kama wasu alburusai kimanin 280.
A cewar kwamishinan kama makaman ya biyo bayan umarnin da babban Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya ya bayar, na cewa duk wasu da ke dauke da makamai su mika su ga ‘yan sanda kafin a fara kamawa tare da hukunta duk wani da aka samu rike da makami ba tare da izini ba.
Daga cikin makaman da rundunar ‘yan sandan ta kama akwai manya-manyan bindigogi da suka hada da AK-47 guda shida da wasu bindigogi da ake wa lakabi da "Pump Action" guda 38 da kuma wasu bindigogi kirar gida.
Haka kuma an kama wasu mutane da ake zargin suna da hannu a mallakar bindigoyin ko kuma aikata wasu munanan aiki a birnin Legas.
A kwanakin baya ne dai babban Sifeto Janar na ‘yan sandan Najeriya, ya bai wa ‘yan Najeriya da ke rike da makamai wa’adin wata guda, da su mikawa ‘yan sanda makamansu.
Wannan umurni na daya daga cikin matakan da hukumomin tsaro ke dauka na raba mutane da makamai, gabannin zabe mai zuwa na 2019.
Domin karin bayani saurari rahotan Babangida Jibrin.
Facebook Forum